(ABNA24.com) Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi hasashen cewa za’a samu raguwar adadin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a Afrika, sannan yanayin kai wa kololuwar cutar zai zo sannu a hankali a galibin kasashen nahiyar.
Daraktar WHO a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce an sake nazarin ne bisa nasarar da aka samu daga wasu matakai da gwamnatoci ke aiwatarwa, kamar wani bangare na matakin kulle da nisantar taron jama'a da wanke hannu.
Ta ce wani nazarin da hukumar ta yi, ya nuna cewa adadin masu kamuwa da COVID-19 a Afrika zai kai matsayin koli cikin makonni 5 da samun bullar cutar na farko a wata kasa, kuma a matsakaicin mataki, kimanin kaso 26 na al'ummar nahiyar, za su kamu da cutar.
Jami'ar ta bayyana cewa, an yi wannan nazari ne bisa la'akari da yanayin yaduwar cutar a cikin al'umma, musammam a yankunan karkara, amma kuma sun ga yadda gwamnatocin nahiyar suka dauki matakai da suka rage yaduwar cutar.
Kawo yanzu dai mutum 81,307 ne Cutar korona ta kama a Afrika, kamar yadda hukumar dakile yaduwar cutuka ta Afrika CDC ta wallafa a shafinta na twitter yau Lahadi.
Kazalika mutum 2,704 sun rasa rayukansu sakamakon annobar, yayin da 31,078 suka warke daga cutar ta covid-19.
/129
18 Mayu 2020 - 04:31
Lambar labari: 1037786
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi hasashen cewa za’a samu raguwar adadin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a Afrika, sannan yanayin kai wa kololuwar cutar zai zo sannu a hankali a galibin kasashen nahiyar.